Kotu ta Tsige Sanata Mai Wakiltar Mazaɓar Arewa maso Gabashin Jihar Akwa Ibom

 

Babbar Kotun tarayya a Abuja ta tsige Sanata mai wakiltar mazaɓar Arewa maso gabashin jihar Akwa Ibom, Albert Akpan

Kotun ta dauki wannan mataki ne bisa hujjar Sanatan ya fita daga PDP babu wani dalili bayan ita ta ɗauki nauyinsa ya ci zaɓe.

Sanata Akpan, ya sauya sheka daga PDP zuwa YPP inda ya samu tikitin takarar gwamna a zaɓe mai zuwa.

Abuja – Babbar Kotun tarayya mai zama a Abuja ta tsige Sanata mai wakiltar Akwa Ibom ta arewa maso gabas, Albert Akpan, sakamakon ficewar da ya yi daga jam’iyyar PDP.

Kotun ta ayyana kujerarsa da wacce babu kowa kana ta umarci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta shirya zaben cike gurbi a mazabar Sanatan cikin kwanaki 14.

Jaridar Prrmium Times ta ruwaito cewa wannan hukuncin ba shi da alaƙa da laifin da Mista Akpan ya aikata na cin hanci wanda Kotu ta tura shi gidan yari kwanakin baya.

Kotu ta tunbuke shi daga kujerar Sanata ne sabida sauya shekar da ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa Young Progressives Party (YPP).

Da take yanke hukunci kan karar da PDP ta shigar, Mai shari’a Faɗima Aminu, ta yanke cewa Mista Akpan bai cancanci cigaba da zama a muƙamin ba bayan ya fita daga jam’iyyar data kai shi ga nasara.

Alkalin ta umarci Akpan da ya daina ayyana kansa a matsayin Sanata kuma ta umarce shi da ya baiwa jam’iyyar PDP mai ƙara miliyan N5m kan sauya shekar da ya yi zuwa YPP.

Mai shari’a Faɗima ta kara da cewa Akpan, sanata tsawon zango biyu, ya gaza kare kansa kan dalilin da ya tilasta masa sauya sheka daga PDP.

Sakamakon rashin gamsasshen jawabi, Alkalin ta ce sauya shekar da ya yi ta saba wa sashi na 68(1)(g) na kundin mulkin Najeriya wanda ya tanadi cewa dole ya bar kujerarsa.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here