Dalilin da Yasa Gwamnatin Kano ta ɗage Ziyarar Shugaba Buhari

 

Gwamnatin Kano ta ɗage ziyarar da shugaban ƙasa Buhari zai kawo Kano domin kaddamar da ayyuka.

A wata sanarwa da gwamnatin ta fitar ta bayyana manyan dalilin da ta hanga ya sa ta ɗauki wannan matakin.

Shugaba Buhari zai kai ziyara don kaddamar da wasu ayyukan Ganduje a Kano tsakanin 30 da 31 ga watan Janairu kafin wannan ci gaban.

Kano – Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, a ranar Asabar, ya rubuta wasika ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, yana neman ya ɗage ziyarar da zai kawo jahar.

Ganduje yace ya nemi haka ne bayan korafin da Kanawa suka yi kan wahalar da suke sha wajen samun sabbin takardun kuɗi, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Gwamnan yace yan majalisun Kano, shugabannin siyasa da ‘yan kasuwa sun goyi bayan matakin ɗage zuwan shugaban ƙasa, ya kuma roki a ƙara wa’adin daina karban tsaffin kuɗi.

A wata sanarwa da hadimin Ganduje, Abba Anwar ya fitar ya ce:

“Saboda wahalar da mutane ke ciki sakamakon ƙarancin wa’adin dena amfani da tsaffin kuɗi na babban bankin CBN, Ganduje ya bayyana cewa Kano ta rubuta wasika zuwa fadar shugaban kasa.”

“Wasikar ta nemi a ɗage ziyarar da shugaban ƙasa kai kawo jihar Kano domin kaddamar da wasu muhimman ayyuka.”

Sanarwan ta kara da cewa an cimma matsayar daukar wannan matakin ne ranar Jumu’a a gidan gwamnati yayin ganawa da Malamai, ‘yan majalisu, shugabannin siyasa da yan kasuwa.

“An ɗauki wannan matakin ne domin gujewa faruwar wani abu da ba’a yi tsammani ba,” a cewar Sanarwan, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa kafin wannan ci gaban, an tsara zuwan shugaban kasan ne a tsakanin Ranakun 30 da 31 ga watan Janairu, 2023 domin ya kaddamar da wasu ayyukan Ganduje.

“Yayin da muke dakon wannan ziyara mun tsinci kanmu a tsaka mai wuya, wanda ya jefa mutanen mu cikim wahala. Dogaro da dalilan tsaro mun nemi shugaban ƙasa ya ɗage ziyarar.”

– Ganduje.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here