Gwamnatin Edo ta Bada Wa’adi ga Masallatai, Coci, Wuraren Shakatawa da su Sanya Na’urorin Daidaita Sauti

 

Za a rufe coci-coci, masallatai, dakunan taro, wuraren shakatawa da kasuwanci ire-iren su a Edo idan ba su daidaita sautin da ke fitowa daga cikinsu ba.

Gwamnatin Jihar Edo ta fitar a wata sanarwa cewa ta bada wa’adin kwana 90 ga masu irin gine-ginen.

Rahotanni sun bayyana cewa wa’adin zai kare ranar Juma’a, 31 ga Maris na 2023.

Edo, Benin – Gwamnatin Jihar Edo ta bada gargadin karshe ga Cocina, Masallatai, wuraren taruka, da gidajen rawa da sauran wuraren shakatawa da ba su sanya na’urorin daidata sauti a gine-ginensu ba.

Kamar yadda Nigerian Tribune ta ruwaito, gwamnatin Jihar tace wa’adin da aka bayar don takaita kara da za ta iya damun mutane zai kare ranar Juma’a, 31 ga watan Maris.

An zartar da matakin ne a wani taro tsakanin masu irin wannan gine-ginen dake da bukatar daidata sauti da kuma gwamnati.

Legit.ng ta tabbatar wata hukumar hadin gwiwa da aka kafa karkashin ma’aikatar tsare-tsare, cigaban birane da gunduma da kuma ma’aikatar muhalli ta tura kashedin karshe ga masu wuraren bauta da kasuwanci kan subi umarmin gwamnatin jihar.

Gwamnatin jihar kamar yadda ta fitar a wata sanarwa ta ce: ”An zartar da hukunci bayan taro tsakanin masu ruwa da tsaki da abin ya shafa da kuma jami’an gwamnati kan bukatar sanya abun da zai takaita tashin kara, wanda aka yi ranar 31 ga Oktoba, 2022.”

Mun tura sanarwa ga wanda abin ya shafa – Gwamnatin Edo

A wani rahoton, kwamishinan MPPHURD, Isoken Omo yace, sanarwar ta kunshi bayanai game da matsayar da aka cimma tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsaki don bin wannan dokar.
Da yake karin haske akan abin da ke kunshe a sanarwar, Isoken Omo ya ce:

”Masu irin wannan waurare suna da wa’adin kwana 90. An kuma makala wata takarda ta take kunshe da irin na’urorin da ya kamata ayi amfani da su, da kuma aikin ma’aikatar muhalli wajen karin bayani akan irin abin da ya kamata ayi amfani da shi.”.

”Anyi hakan dan takaita sakin kara barkatai zuwa yadda bazai dami mutane ba kamar yadda kunshe cikin dokar Muhalli ta kasa, mai lamba F.R.N part V 13-1308 17 – (2) da kuma dokikin tsara birane. Hakan kuma ya zama dole bayan da MPPHURD ta karfi dumbin korafi da kuma kararraki daga al’umma.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here