Kotu ta yi Watsi da ƙarar Gaya ta Bai wa Sumaila Nasara

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya a jihar Kano, ta zartar da hukunci kan ƙarar zaɓen sanatan Kano ta Kudu.

Kotun ta yi fatali da ƙarar da Kabiru Gaya na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya shigar yana ƙalubalantar nasarar Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP.

A cewar mai shari’a R.O Odogu kotun ta yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancantar ta inda ta umarci mai shigar da ƙara ya ba wanda ake ƙara N200,000.

Jihar Kano – Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya mai zamanta a birnin Kano, babban birnin jihar Kano ta yi watsi da ƙarar Kabiru Ibrahim Gaya na jam’iyyar All Progressive Congress (APC).

Kabiru Gaya ya shigar da ƙarar ne yana ƙalubalantar nasarar da Abdulrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya samu a zaɓen sanatan Kano ta Kudu.

Meyasa kotu ta yi fatali da ƙarar?

Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen dai ta yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancantar ta, cewar rahoton Daily Trust.

Kotun mai alƙalai uku wacce mai shari’a R.O. Odogu yake jagoranta ta yi hukunci cewa mai shigar da ƙarar ya kasa sauke nauyin da ke kansa na kawo hujjoji akan wanda ya lashe zaɓen.

Mai shari’a Odogu ya bayyana cewa sun yi fatali da ƙarar ne saboda rashin cancantar ta, rahoton Leadership ya tabbatar.

A kalamansa:

“Ba mu ga wata cancanta a cikin wannan ƙarar ba, saboda haka, mun yi watsi da ita. Hakazalika mun sake tabbatar da ayyana Abdulrahman Kawu Sumaila na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaɓen kujerar Sanatan Kano ta Kudu da aka gudanar a ranar 25 ga Fabrairun 2023.”

Kotu ta kuma umarci masu shigar da ƙara su biya waɗanda ake ƙara tsabar kuɗi N200,000.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com