Hukuncin Kisa: Kotun Sojoji ta Yankewa Sojan da Ya Kashe Kwamandansa
Kotun sojoji dake zamanta a Maiduguri, jahar Borno ta yankewa jami’in soja, Azunna Maduabuchi hukuncin kisa kan laifin kisan kwamandansa, Laftanal Babakaka Ngorji.
Kotun ta yanke a kashe shi ta hanyar harbi, Channels Tv ta ruwaito.
An gurfanar da Maduabuchi ne bayan da ya budewa Babakaka Ngorji wuta a watan Yulin 2020 a sansaninsu dake karamar hukumar Bama a jahar Borno don ya hanashi zuwa gida.
Read Also:
Kotun dake Maimalari Cantonment, ta kamashi da laifin kisan kuma ta yanke masa hukuncin kisa.
Sauran sojojin da aka kama da laifin kisa sun samu hukuncin dauri shekaru a gidan kaso.
Wadanda aka yankewa hukumar sune Sajen Sani Ishaya, hukucin shekaru hudu; Bidemi Fabiyi, hukuncin shekaru biyu; sai kuma Private Musa Bala da Abdulrasheed Adamu, da aka yankewa hukuncin shekara daya.
Wani Soja kuma mai suna Mohammed Kudu da aka tuhuma da laifin kashe wani yaro a wani bikin daurin aure ya samu daurin shekaru uku a gidan kaso. Hakazalika an ragewa Lance Kofura Aja Emmanuel matsayi kan laifin cin zarafi. Yanzu ya koma Private.