Daddy Hezekiah ya yi Kira ga Gwamnatin Najeriya Kan Cin Bashin Kasar Sin

Shugaban cocin Living Christ Mission Incorporated ya soki Gwamnatin APC

Daddy Hezekiah ya ce karbo bashi daga hannun Gwamnatin Sin ya na da illa.

Faston ya ce an murde zaben Amurka, ya yi kira ayi wa Donald Trump addua.

Shugaban cocin Living Christ Mission Incorporated, Daddy Hezekiah, ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta daina cin bashi daga kasar China.

Farfesa Daddy Hezekiah wanda shi ne wanda ya kafa jami’ar Daddy Hezekiah da ke jahar Imo, ya ce cin bashi musamman daga Sin yana da matukar hadari.

Jaridar Vanguard ta rahoto Daddy Hezekiah ya na sukar yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ke rabon mukaman mukarraban na kusa da shi.

Faston yace muddin gwamnatin APC mai mulki ba ta canza salo na son kai wajen rabon kujeru ba, abubuwa ba za su dawo daidai a kasar nan ba.

Gwamnatin APC a Najeriya ba ta da wata daraja, kuma mutane masu daraja ne kawai za su iya ceto Najeriya daga halin da ta ke ciki a dalilin jam’iyyar da ke mulki.”

A cewar Hezekiah, ana bukatar ayi wa tsarin Najeriya garambawul kafin a ci moriyar arzikin al’umma da albarkatun da kasar ta ke da shi.

Da ya ke magana, Fasto Hezekiah ya tofa albarkacin bakinsa game da zaben kasar Amurka, ya ce an yi magudi a zaben 2020 wanda Donald Trump ya sha kasa.

Faston ya ce zaben abin kunya ne ga kasar Amurka da ta zama abin koyi ga Duniya. Hezekiah ya ce nasarar Joe Biden hadari ne saboda goyon bayan auren jinsi.

Farfesan ya yi kira ga kiristoci su yi wa Donald Trump addua’a, ya soki tafiyar tsohon shugaban kasar Amurka Barack Obama da manufofinsa na ‘shaidanci’.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here