kuɗin Corona: Ka Binciki Gwaman Kogi Kan Yadda Akai da N4.5b – SERAP ga Shugaba Buhari

 

Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin Bil’adama SERAP ta roki shugaba Buhari ya gudanar da binciki kan yadda aka kashe 4.5 Biliyan na COVID19 a jahar Kogi

SERAP ta ce ya kamata gwamnan jahar Yahaya Bello ya fito ya yi bayanin yadda aka karkatar da kuɗaɗen.

Shi dai gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa babu cutar kwata-kwata a jahar sa.

Ƙungiyar dake fafutukar kare haƙƙin bil’adama da saka ido kan al’amuran kuɗi (SERAP) ta roƙi shugaba Buhari ya yi bincike kan yadda aka karkatar da 4.5 biliyan kuɗin korona.

Gwamnatin tarayya ta tura ma gwamnatin jahar Kogi 4.5 miliyan da ta samu daga rance, da kuma gudummuwa da ta samu don yaƙi da cutar COVID-19, PM News ta ruwaito.

SERAP ta bayyana haka ne a wani jawabi da ta fitar ranar Asabar. Ta roƙi shugaba Buhari da yaba Ministan shari’a da sauran hukumomin da ke yaki da cin hanci da rashawa umarnin bincikar yadda aka ƙasafta kuɗin.

A jawabin SERAP ta ce:

“Da zarar an sami ƙwaƙƙwarar shaida, duk wanda ake zargi a hukunta shi dai-dai da abinda ya aikata.”

A jawabin Mataimakin shugaban Ƙungiyar, Kolawole Oluwadare, ya sama hannu ya bayyana cewa:

“Bada umarnin ga ministan shari’a da kuma sauran hukumomin yaƙi da cin hanci doka ce a kundin tsarin mulkin ƙasar nan.”

Kuma idan shugaba Buhari ya bada wannan umarnin to yana ƙara tabbatar da bayanin da ya yi lokacin rantsar dashi “Zan tabbatar da duk wasu ayyuka an gudanar da su yadda ya kamata a dukkan matakan gwamnati” inji Buhari.

“Kamar yadda ka faɗa a wancan lokaci, ya zama wajibi gwamnatinka ta faɗaɗa yaƙi da cin hanci da rashawar da take yi zuwa dukkan matakan gwamnati uku da muke da su,” cewar SERAP ga Buhari.

Ƙungiyar tace ta damu da yawan korafe-korafe kan cin hanci da rashawa da kuma amfani da kuɗaɗen gwamnati ta inda bai kamata ba a dukkan jahohin Najeriya.

Ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki na yin bincike zai ƙara tabbatar da gaskiya da riƙon amanar gwamnati wadda ta ƙunshi jahar Kogi.

“Zami matukar jin daɗi idan aka ɗauki mataki akan korafin mu cikin kwanaki 14 da turo shi. Idan kuma ba ayi komai ba bayan wannan lokacin, SERAP zata ɗauki matakin da doka ta tanadar wajen ƙalubalantar gwamnati har ta yi abinda ya dace.” Cewar SERAP.

SERAP ta tura cikakken bayanin da tayi a jawabinta zuwa ofishin ministan shari’a, Abubakar Malami, shugaban ICPC, Professor Bolaji Owasanoye, da kuma shugaban Hukumar yaƙi da cin hanci ta ƙasa (EFCC) Abdulrasheed Bawa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here