Dakarun Afrika ta Kudu Sun Kubutar da Ministocin da Aka yi Garkuwa da su
Dakaru na musaman a Afrika ta Kudu sun kubutar da wasu ministocin gwamnati biyu da wani mataimakin minista da tsoffafin mayakan da suka yi gwagwamayar kawar da wariyar launin fata suka yi garkuwa da su.
Wadanda ake zargin na neman a biya su diyya ne game da rawar da suka ce ‘yan siyasar sun taka a wariyar launin fata.
Tsofaffin mayakan da suka fito daga wani reshe na sojojin jamiyyar ANC da aka rusa sun tattauna da Ministar Tsaro ta Afrika ta Kudun, Thandi Mondise, da wani minista a fadar shugaban kasa a wani otel da ke kusa da Pretoria.
Rahotanni na cewa tsoffafin mayakan da ake kira Liberation Struggle War Veterans sun bukaci a biya su diyyar dala 280,000 da inshorar gida da kuma ta lafiya ga iyalansu.
Sun hana ministocin barin wurin ne bayan da suka kasa cimma matsaya a tattaunawar ta su.
‘Yan sanda sun ce an kama mutane sama da 50 bayan an aka kasa samun nasara a tattaunawar neman sakin wadanda ake garkuwa da su.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here