Jerin Kudade Mafi Munin Daraja a Nahiyar Afrika a 2022
Kudin Najeriya, wato Naira ya shiga jerin kudade mafi muni a nahiyar Afrika a shekarar nan ta 2022.
Kudaden kasashe bakwai ne suka shiga wannan jeri, wanda suka shaida raguwar daraja a tsawon lokaci.
A jerin kudaden, kudin kasar Zimbabwe ne na farko a jerin kudaden mafi munin daraja a jerin kudade bakwai.
Steve Hanke, farfesan tattalin arziki kuma daraktan Troubled Currencies Project a kasar Amurka ya buga wani rahoton mako mai nuna kudaden da suka gamu da raguwar daraja da akalla 20% na dalar Amurka.
Hanke ya bayyana cewa, kudaden da ya tattaro a jerinsa sun gamu da raguwar daraja ne cikin shekaru biyu kacal.
Business Insider ta ruwaito cewa, wannan jeri na Hanke ya nuna adadin hauhawar farashin kayayyaki da kuma raguwar darajar kudi a kasashen.
Dalar Zimbabwean
A jerin Hanke, kudin kasar Zimbabwean ne kan gaba a kudaden da basu da daraja a nahiyar Afrika.
Daga Janairun 2020 zuwa yanzu, dalar Zimbabwe ya rage dajara da 97.33%. Hanke ya ba kasar shawarin yin watsi da kudinta tare da kama amfani da dalar Amurka nan take.
Pound na kasar Sudan
Kudin kasar Sudan ne na biyu a jerin kudade mafi munin daraja a Afrika, kuma ta ga taskun ragin daraja daga 2020 zuwa yanzu da 84.95%.
Read Also:
Hanke ya shawarci kasar Sudan da ta gaggauta kirkirar hukuma kan harkokin kudi don ceto darajar kudinta.
Pound na Kudancin Sudan
Wannan kudi dai ya ga tasku, domin ragin darajar 50.79% ya samu a cikin shekaru biyu kacal.
Naira
Kudin Najeriya, wato Naira, shine na hudu a jerin Hanke kuma na 11 a jerin kudaden duniya mafi munin daraja.
Naira ta Najeriya ta rasa 48.87% na daraja a cikin shekaru biyu kacal.
Rahoton Bloomberg ya ce, Naira ta shiga jerin kudade mafi muni a duniya, inda aka jero kudaden kasashe 148 na duniya.
Hakazalika, rahoton na Bloomberg ya ce Naira dai bata samu wani tsaiko ba saboda 4% kadai ta rage daraja idan aka kwatanta da darajar dala da sauran kudaden duniya
Cedi na kasar Ghana
Kudin kasar Ghana, Cedi ne na biyar a jerin Hanke na kudade mafi munin daraja a nahiyar Afrika.
Ya samu raguwar daraja da 42.57% idan aka kwatanta da dalar Amurka a cikin shekaru biyu kacal.
Kwacha na Malawi
A baya na daga cikin kudade mafi daraja a Afrika, a yanzu kuwa Kwacha ya shiga jerin kudade mafi munin daraja a nahiyar ta Afrika.
Ya samu raguwar daraja da 39.54% idan aka kwatanta da dalar Amurka cikin shekaru iyu kacal
Leone na kasar Saliyo
Na bakwai a jerin kudade mafi munin daraja a Afrika, kudin kasar Saliyo kenan.
Ya samu ragin 31.23% na daraja idan aka kwatanta da dalar Amurka daga Janairun 2020 zuwa yanzu.