Ashiru Kudan ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Zuwa ADC
Tsohon dan takarar gwamnan jihar Kaduna na jam’iyyar PDP, Isa Ashiru Kudan ya fice daga jam’iyyar.
Read Also:
Cikin wata sanarwa da ya fitar, Ashiru ya ce ya auki matakin ne sakamakon rigingimun da ya ce jam’iyyar na fama da su.
Ashiru ne ya zo na biyu a zaɓen gwamnan jihar Kaduna na 2023.
Ficewar ta sa na zuwa ne a daidai lokacin da siyasar Najeriya ta fara ɗaukar ɗumi.
A baya-bayan nan jam’iyyar APC ta ADC na ci gaba da jan sabbin magiya baya, inda mutane daga jam’iyyu daban-dban ke komawa cikinsu.















