2023: Kudi na ke Bukata ba Kujerar Shugaban Kasa ba – Rotimi Amaechi ga Magoya Bayansa
Rotimi Amaechi, Ministan Sufuri (Dan Amanar Daura) ya shaida wa magoya bayansa cewa shi fa yanzu kudi kawai ya ke bukata domin ya kula da kansa.
Ya yi wannan furucin ne yayin martani ga wasu kungiyoyin magoya bayansa da suka bukaci jam’iyyar mai mulki ta APC ta bashi tikitin takarar shugaban kasa a 2023.
Duk da hakan, wasu rahotanni sun nuna cewa an hangi fastocin takarar shugabancin kasa na Amaechi a wurin taron gangamin APC da aka yi a ranar Asabar.
Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, yayin da ya ke karyata jita-jitar cewa zai fito takarar shugaban kasa a 2023, ya bukaci magoya bayansa su bashi kudi a maimakon kujerar shugabancin kasar.
Read Also:
Idan za a tuna, The Punch ta rahoto cewa wata kungiya, Amaechi Vanguard a Amurka da Canada, ta bukaci jam’iyyar na APC ta zabi Amaechi a matsayin dan takarar jam’iyyar na shugaban kasa a 2023.
A bangarensa, Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya ce zai iya yin takarar shugabancin kasa a 2023 ne, a matsayin shugaban kasa ko mataimaki tare da Amaechi, idan Shugaba Buhari ya dage kan hakan.
Kudi na ke bukata ba kujerar shugaban kasa ba, Amaechi
Amaechi, yayin martaninsa game da bukatar ya fito takarar, ya ce abin da ya ke bukata kawai shine kudi da zai kula da kansa ba shugabancin kasa ba.
Da ya ke magana a Arise TV, ya ce:
“Mutanen da ke son in yi takarar shugabancin kasa a 2023, su bani kudi kawai. Ina bukatar kudi domin in kula da kai na.”
Amma, wasu rahotanni sun nuna cewa an ga hotunan takarar shugabancin kasa na Amaechi a wurare da dama a Eagles Square, inda aka yi taron gangamin jam’iyyar APC a ranar Asabar.