Duk Wani Taro da Bishop Kukah Zai Shirya ya Zama na Hadin Kai ba Janyo Tsanar Juna ba – Sarkin Musulmai
Sarkin Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar ya jagoranci JNI, inda suka yi wa shugaban kirista na Sokoto kaca-kaca.
Sun caccake shi kwarai a kan taron da ya shirya na kirsimeti, inda suka ce ya yi ne don cin mutuncin Musulunci da Musulmai.
Kamar yadda sarkin yace, ya kamata duk wani taro da Bishop Kukah zai shirya ya zama na hadin kai ba janyo tsanar juna ba.
Sarkin Sokoto, Alhaji Sa’ad Abubakar ya jagoranci JNI a ranar Laraba inda suka yi wa shugaban addinin Kirista na yankin jihar Sokoto, Bishop Matthew Kuka, wankin babban bargo akan taron da ya shirya a ranar Kirsimeti.
Kungiyar ta kwatanta taron Kirsimetin da Kukah ya tattara a matsayin kibiya mai dafi da ya harba ga Musulunci da Musulman kasar Najeriya, The Cable ta ruwaito.
A wata takardar JNI da suka saki bayan makonni 3 da Bishop din ya tura wani sako ga shugaba Muhammadu Buhari, wanda yake zarginsa da son kai da wariya.
Read Also:
Bayan nan ne, a ranar Laraba a jihar Kaduna, JNI ta saki wata takarda wacce ta caccaki taron da Kukah ya tara na kirsimeti, wacce sakataren JNI, Dr Khalid Abubakar Aliyu, ya sanya hannu, inda yake kwatanta taron da Kukah yake shiryawa a matsayin “mara amfani kuma taron bore ga gwamnati.”
Kamar yadda wani bangare na takardar yazo, “Duk da dai sakon Kukah ya fake ne da siyasa don a bata tunanin wadanda basu ji ba, basu gani ba, amma tabbas wannan an yi shi ne don ya harbi zuciyar musulunci da musulman Najeriya da gurbataciyar kibiya, a dalilin haka ya kamata mu sanya baki.
“Hakika Bishop din ya shirya maganganu ne musamman saboda taron da kuma jama’ar da za su taru; wajibi ne a yarda cewa an yi ne don cin zarafin musulunci ta wata kebantacciyar hanya. “Ya yi kokarin zagin musulmai a boye don ya janyo tsana da kiyayya a garesu.
“Kamata yayi ace duk taron kirsimeti za a yi shi ne don janyo so, kauna, hadin kai, yafiya da janyo juna a jiki musamman ta hanyar addu’a a wannan lokaci mai tsanani.”