Donald Trump ya Yarda Zai Sauka Daga kan Mulki

 

Daga karshe, shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya amince zai sauka daga mulki kuma ya mikawa Joe Biden bayan majalisar dokoki ta rattaba hannu kan sakamakon zaben.

Amma duk da amincewa da mika mulki, Trump ya jaddada cewa lallai an yi masa magudi ne kuma shi ne sahihin wanda ya lashe zaben.

Ya jaddada cewa bai amince da sakamakon zabe ba, duk da cewa babu wata hujjar da ta nuna cewa an yi magudi.

Jawabin yace: “Duk da cewa sam ban amince da sakamakon zaben ba, kuma ina da hujjoji, zan mika mulki ranar 20 ga Junairu.”

“Tuni na lashi takobin cewa ba zamu yarda ba kuma sahihan kuri’u kadai za’a kirga.”

“Yayinda wannan ya kawo karshen mulkin shugaba mafi inganci a tarihi, yanzu muka fara yakin sake kara girman Amurka.”

Saurari karin bayani…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here