Kungiyar Kiristoci ta CACN ta Fara Bayar da Katin Shaida ga Malamanta

 

Wata kungiyar addini da aka fi sani da kungiyar limaman addinin Kirista a Najeriya (CACN) ta sanar da matakin bayar da katin shaida ga malamanta a Najeriya.

Kungiyar ta bayyana cewa ta dauki matakin ne sakamakon martani daga abin kunyar da wasu bishop suka ja wa kiristoci a wajen kaddamar da dan takarar mataimakin shugaban kasa na APC.

CACN ta yi la’akari da cewa kwararrun kungiyoyi irinsu NBA da ma na likitocin kasar suna da katunan tantance mambobi don haka, babu abin da ya isa ya hana malamai yin haka.

Onitsha, jihar Anambra – Kungiyar malaman addinin Kirista a Najeriya ta fara ba da katunan tantance ga daukacin malaman addinin Kirista a kasar.

Kungiyar ta ce bayyanar wasu mutane sanye da tufafin bishop yayin bikin kaddamar da mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Kashim Shettima, a Abuja kwanan nan ne ya jawo hakan.

Ta ce irin martanin da wannan lamarin ya haifar da kuma abin kunyar da ya haifar ga kungiyar Kiristoci ta Najeriya ya sa ya zama wajibi a fara bayar da katin ga dukkan limaman Kirista a Najeriya domin a samu sauki wurin tantance su.

Ko’odinetan CACN na kasa, Mai Shari’a Alpha Ikpeama, da Sakatarenta na kasa, Bishop Joseph Ajujungwa, ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwar hadin gwiwa da aka ba manema labarai a Onitsha ta jihar Anambra, ranar Laraba.

Sun ce za a gudanar da atisayen ne tare da hadin gwiwar kafafen yada labarai na Bible Family Christian Media da aka fi sani da Bible Media, cibiyar bincike da yada labaran kiristoci ta duniya.

Kungiyar ta yi nuni da cewa, idan kwararrun kungiyoyi, kamar kungiyar lauyoyi ta Najeriya da kuma likitocin kasar suna da katunan tantance mambobi, babu abin da zai hana malamai yin hakan.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here