Kutsen DSS a Gidan Igboho: Kotun Jahar Ibadan ta Yarda da Bidiyoyin Shaida da Aka Mika Gaban ta

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zama a Ibadan ta aminta da bidiyoyin da lauyan Igboho ya mika na kutsen DSS a gidansa.

Har ila yau, kotun ta amince da cewa bidiyon da DSS ta mika ta lalata shi, lamarin da yasa ta fara kare kan ta.

Sai dai kuma lauyoyin Malami da na DSS sun ce ya zama dole a je a gwada jinin da aka gani a bidiyon don tabbatar da cewa na mutum ne ko dabba.

Ibadan – Wata babbar kotun da ke zama a Ibadan a ranar Talata ta yarda da bidiyoyin shaida da aka mika gaban ta kan zargin kutsen da jami’an tsaron farin kaya suka yi a gidan Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho a ranar 1 ga watan Yuli.

Kamar yadda Daily Nigerian ta wallafa, lauyan Igboho, Yomi Aliyu, SAN, ya mika kara tare da bukatar a biya shi diyyar biliyan N500 daga wurin antoni janar na tarayya, Abubakar Malami, SSS da kuma daraktan DSS na jahar Oyo a kan kutse.

Tun farko Aliyu ya sanar da kotun cewa, an kutsa gidan wanda ya ke karewa da motocinsa kuma an ragargaza tare da kashe wasu mutum biyu.

A zaman ranar Talata, Mai shari’a Ladiran Akintola, ya yarda da shaidun da aka mika gabansa bayan Aliyu ya bayyana asalin dalilin da yasa suka gurfana a gaban kotu, Daily Nigerian ta wallafa.

Akintola ya sake yadda da bidiyon da lauyan DSS ya mika, T. A. Nurudeen, inda Igboho ke barazanar kafar jamhuriyar Oduduwa, balle wa daga Najeriya da kuma kiran Yarabawa da su kare kan su da layu da bindigogi.

Kotun ta bukaci a saka bidiyoyin biyu a bayyane a kotu kamar yadda lauyan Igboho da na SSS suka bukata.

A yayin jawabi ga kotun bayan an saka bidiyoyin, lauyan AGF, Abdullah Abubakar, ya ce ba bu shaida a gaban kotu kan cewa jinin da aka gani a bidiyon ko na mutum ne.

Abubakar ya kara da cewa, babu wani abu a bidiyon da ya nuna cewa gidan da aka kutsa na Igboho ne ko kuma kutsen ya na da alaka da AGF. Don haka ya yi kira ga kotun da ta yi watsi da duk wata shaida tare da korar karar da aka shigar.

Lauyan SSS, Nurudeen, ya ce tabbas ya zama wajibi likitoci masana halittar jini su tabbatar da cewa wannan jinin na mutum ne ba na mage ba.

Akintola ya dage sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Satumba domin yanke hukunci.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here