‘Yan Bindiga 50 Sun Mutu: Jirgin Yakin Sojojin Saman Najeriya ya Kona Sansanin ‘Yan Bindiga a Dajin Kawara Dake Kaduna

 

Jirgin yakin dakarun sojojin Najeriya na sama ya ragargaji wani sansanin kuma ma’adanar ‘yan bindiga a dajin Kawara, jahar Kaduna.

Jirgin yakin ya hango miyagun tare da shanun sata sanye da bakaken kaya, hakan yasa aka harba musu bama-bamai da suka tashi da su.

Jirgin ya hango wata ma’adanarsu inda ya jefa bam ta kone babura tare da kayan abinci, an samu gawawwaki a kalla 50 na miyagun.

Kaduna – A sakamakon tashi tsaye da gwamnati ta yi wurin kawo karshen ta’addanci a wasu jahohin arewa, dakarun sojoji suna ta kai da kawowa tsakanin Zamfara zuwa wasu jahohi a cikin kwanakin nan.

Sojojin saman Najeriya sun yi nasarar kone wani sansanin ‘yan fashin daji da ke jahar Kaduna.

Kamar yadda PRNigeria ta tattaro, miyagun suna amfani da sansanin wurin buya a dajin Kawara da ke karamar hukumar Giwa ta jahar Kaduna.

Majiyoyi sun kara da cewa, a kalla ‘yan fashin daji 50 sun sheka lahira bayan bama-baman da dakarun suka sakarwa miyagun, Daily Trust ta rawaito.

Kamar yadda wata majiya ta cikin dakarun sojojin saman ta sanar, jirgin yakin NAF ya tare wasu tarin ‘yan fashin daji da ke sanye da bakaken kaya kuma sun sato shanu wurin kauyen Kawara a karamar hukumar Giwa ta jahar Kaduna.

“Bayan sun hango jirgin yaki, ‘yan bindigan sun tsere tare da boyewa cikin shanun yayin da suke neman hanyar gudu.

“Bayan hadewa da suka yi a wurin wani ruwa za su tsallaka, an yi nasarar jefa musu bam ta jirgin yakin. “An hango gawawwakin wasu daga cikin ‘yan fashin dajin yayin da wasu da ke kokarin tserewa aka sake sakar musu bam.

“Bayan an sake duba daga inda suka fito, an hango wani sansani da suke adana kayan ayyukansu wanda aka sakar masa bam ya kone kurmus.

“Majiyoyi daga kasa a Kawara a ranar Litinin sun tabbatar da cewa a kalla gawawwakin miyagu 50 aka kirga yayin da aka tsinci babura da kayan abinci konannu a sansanin,” ya ce.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here