Iyakar Amurka da Mexico: An Kwashe Mutanen da Suka Yada Zango a ƙarƙashin Gada
An kwashe ɗaruruwan mutanen da suka yada zango ƙarƙashin wata gada da ke iyakar Amurka da Mexico da niyyar shiga Amurka a matsayin ƴan ci rani inda aka mayar da su ƙasarsu ta Haiti.
Read Also:
Jami’an hukumar kula da shige da ficen Amurka ba su yi ƙarin haske kan lamarin ba, sai dai rahotanni na cewa an cika jirage uku taf da jama’a inda aka mayar da su Haiti.
Sai dai babban jami’in masu kula da iyakar Amurka Raul Ortiz cewa ya yi, “abin da muke sa rai shi ne mu kwashe ƴan ci rani sama da 3,000 daga ƙarƙashin gada zuwa wurin da za mu tantance su ko kuma wurin da za su hau jirgi nan da awa 24.
Sama da mutum 13,000 ne wadanda akasari ƴan Haiti suka taru a ƙarƙashin gada a birnin Del Rio da ke kan iyakar Amurka da Mexico.