ƙyandar Biri : Mutune 157 Sun Kamu da Cutar a Najeriya, Biyar Sun Mutu

 

Hukumar kiyaye yaɗuwar cututtuka ta Najeriya ta tabbatar da cewa mutum 157 sun kamu da cutar ƙyandar biri zuwa yanzu a faɗin ƙasar, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

NCDC ta bayyana hakan ne a rahotonta na baya-bayan nan na mako 30 tun bayan fitowar cutar.

Sannan ta ce mutum biyar cutar ta kashe zuwa yanzu.

Cutar kyandar biri wata cuta ce da ba ta fiye fitowa ba, wadda ke yaɗuwa daga dabbobi zuwa bil-adama, mafi yawanci a kauyuka da ke yankunan tsakiya da yammacin Afirka kusa da manyan gandun daji masu zafi da ruwan sama mai yawa.

Najeriya na ɗaya daga cikin kasashen da cutar ke yaɗuwa a cikinta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here