AU ta Bayyana Cewa ba za ta Lamunci Batun Juyin Mulki a Wasu ƙasashen Afrika ba

 

Kungiyar haɗin kan Afrika ta sake nanata kudurinta na cewa ba za ta lamunci yin katsalandan ga dimokuraɗiyya ba da kuma sauya gwamnatoci da ke mulki a wasu ƙasashe a nahiyar ta hanyar yin juyin mulki.

A rana ta ƙarshe ta taron yini biyu da AU ta yi a Addis Ababa, ta ce dakatarwan da ta yi wa ƙasashen Burkina Faso da Guinea da Mali da kuma Sudan yana nan daram – wanda ƙasashe ne da sojoji ke rike da iko bayan yin juyin mulki.

Kwamishinan harkokin siyasa, Bankole Adeoye, ya ce kungiyar a shirye take domin taimaka wa ƙasashen koma wa kan tsari na mulkin dimokuraɗiyya.

Shugabanni da suka halarci taron, sun kuma amince da batun tsarin kasuwanci maras shinge wanda ya kunshi dukkan ƙasashe a nahiyar ta Afirka.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here