Dalilin da Yasa Gyaran Lantarkin Arewa ya ɗauki Tsawon Lokaci – TCN

 

Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya ya bayyana cewa aikin gyara layin samar da lantarki na Apir-Ugaji ya ɗauki tsawon lokaci ba a kammala ba ne saboda matsalar tsaro a yankin.

Da yake magana a wani taron manema labarai a yau Talata, Manajan Darektan, kamfanin Injiniya Abdulaziz Sule, ya ce injiniyoyin da ke gyaran suna aiki ne bisa kulawar jami’an tsaro -sojoji, kuma da zarar ƙarfe 6 na yamma ya yi dole ne su bar wajen su je wajen da babu matsalar tsaro su kwana sannan da safe su koma bakin aiki.

Amma duk da haka ya ce, za a kammala aikin a cikin kwana biyu ko uku a hanyar wadda take da wani layin na samar da lantarki ga Kano da sauran manyan birane a arewacin Najeriya.

Shugaban ya kuma ce shi ma layin na biyu wanda aka lalata wajen turakuna biyar nasa zai dawo bakin aiki aƙalla zuwa ranar Lahadi – cikin kwana biyar kenan.

Injiniya Sule ya ƙara da cewa da zarar an kammala gyaran layukan biyu, za a iya aikawa da wutar lantarkin da aƙalla ta kai yawan megawatt 500 zuwa 600 ga yankin arewacin Najeriyar.

A kan abin da kamfanin yake yi kuma don hana ɓarnata kayan samar da wutar lantarkin, ya ce suna haɗa kai da al’ummomin yankunan, inda har ma suna ba su kuɗin sufuri da kuma waya don sheda msu duk wani abu da suka gani da zai yi illa ga layukan samar da wutar.

Sannan ya ce suna kuma haɗa kai da jami’an tsaro – sojoji da ‘yansanda da rundunar tsaro da kai ɗauki (Civil_Defense…), domin tabbatar da ganin suna sintiri a wuraren kayan samar da lantarkin.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here