Tabbas Muna so mu Lashe AFCON – Oshimhen

Bayan da Najeriya ta samu galaba a kan mai masaukin baki Ivory Coast da ci daya me ban haushi a gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika watau Afcon, da dama na cewa tawagar Super Eagles ta ba da mamaki.

Nasarar na nufin cewa Najeriya ta farfado da kimarta a wannan gasar.

Bayan kammala wasan, tauraron dan kwallon Najeriya, Victor Osimhen ya tattauna da manema labarai, ga abin da ya ce:

Tambaya: Victor ka gaya mana yaya kake ji game da wannan wasan.

Osimhen: Ina cikin farin ciki, wannan nasara ce mai muhimmanci kuma mun nuna wa ƙasashe ƙarfinmu, gaskiya na ji daɗi sosai. Kasancewar ba mu yi abin kirki ba inda muka ɓarar da maki a wasan farko da Equatorial Guinea, abu ne mai muhimmanci mu fito mu doke ƙasa kamar Ivory Coast kuma ina yi wa tawagarmu murna.

Tambaya: Me kuka yi na daban?

Osimhen: Mun karanci yadda suke buga wasa, muka yi shawarar cewa kar mu hanzarta kai musu hari mu jira su a tsakiyar fili su fito, ina ga abin da ya ba mu damar kai hari ragarsu ke nan.

Tambaya: Za ka iya cewa kun ɗauki hanyar cin wannan kofi?

Osimhen: Yanzu dai muna tafiya a hankali wasa bayan wasa, abu ne me muhimmanci mu ci wasan gaba don zama na ɗaya a rukuninmu. Ba zai yi sauƙi ba tabbas muna so mu lashe AFCON amma a hankali za mu kai wajen. Ni ban damu ba ina da ƙarfin zuciya ko da na ɓarar da ƙwallo ko na ci abu ne da aka saba a ƙwallon ƙafa, bai dame ni ba amma (Troost) ya buga kuma ya ci kuma ya nuna iya jagoranci a gaskiya ban damu ba nasarar ƙasar ce ta dame ni.

Tambaya: Wannan ne karon farko da ka lashe kyautar ‘Man Of The Match’, ya ka ji?

Osimhen: Na ji daɗi kuma na sadaukar da wannan kambi ga ƴan ƙungiyarmu saboda sun yi iya ƙoƙarinsu su ga mun yi nasara wanda shi ya fi muhimmanci.

Tambaya: Kun canja formation zuwa 343 kana ganin dama za ku ci?

Osimhen: Ƙwarai kuwa! Mun shafe kwana biyu muna aiki kan wannan har muka ƙware, ban san dai wanne kocinmu zai ce mu yi amfani da shi a wasan gaba ba amma ni ina son wannan, yana sa ku gano abin da muke buƙata daga juna.

A ranar Litinin 22 ga watan Janairu ne Najeriya za ta buga wasanta na gaba inda za ta fuskanci Guinea-Bissau.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com