Zanga-Zanga: An Katse Hanyoyin Sadarwa na Intanet a ƙasar Comoros

 

Hukumomin ƙasar Comoros sun katse hanyoyin sadarwa na intanet sakamakon zanga-zangar adawa da sake zaben shugaba Azali Assoumani.

An bayar da rahoton mutuwar mutum daya tare da jikkata wasu shida yayin da ‘yan sanda ke ci gaba da fafatawa da fusatattun magoya bayan ‘yan adawa a Moroni, babban birnin kasar.

An killace tituna da dama a babban birnin kasar tare da kama wasu masu zanga-zangar da ba a tantance adadinsu ba.

An kafa dokar hana fitar dare domin daƙile tashe-tashen hankula da ke yaɗuwa.

A ranar Talata ne hukumar zaɓen kasar ta sanar da cewa Assoumani ya samu kashi 63 cikin 100 na kuri’un da aka kada a ranar Lahadi domin tabbatar da wa’adinsa na hudu a matsayin shugaban kasar.

Sanarwar sakamakon zaɓen ta haifar da zanga-zanga a ranar Laraba bayan da jam’iyyun adawa suka ce an tafka maguɗi tare da yin kira da a soke zaɓen.

An lalata gine-gine a babban birnin ƙasar ta hanyar kone-kone, ciki har da gidan wani minista.

Ayyukan Intanet sun lalace sosai kuma ba a iya shiga wasu rukunin intanet, kamar yadda shafin sa ido na intanet na duniya Netblocks ya tabbatar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com