Adadin Waɗanda Suka Mutu Sakamakon Fashewar Nakiya a Ibadan

 

Adadin waɗanda suka mutu sakamakon fashewar nakiya da ya afku a Ibadan, babban birnin jihar Oyo a ranar Talata, 16 ga watan Janairu, ya ƙaru zuwa biyar, in ji gwamnatin jihar.

An lalata gidaje da dama sakamakon fashewar, wadda ta kai tsawon kilomita 14.

A daren jiya, gwamnan jihar, Seyi Makinde, yayin da yake bayar da ƙarin haske a gidan talabijin na Channels, ya ce an samu rahoton mutuwar mutane biyu a ranar Talata, inda ya ƙara da cewa wani wanda abin ya shafa ya mutu a asibiti ranar Laraba.

Sai dai a wani sabon rahoto da aka fitar a ranar Alhamis, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin tsaro, Fatai Owoseni, ya ce an sake gano wasu gawarwaki biyu.

“Har yanzu ana ci gaba da aikin ceto. Ya zuwa jiya, mun samu waɗanda suka samu raunuka uku amma da safiyar yau, na samu labari daga jami’an tsaro da ke tallafa wa tawagar likitoci cewa an sake gano wasu gawarwaki biyu” kamar yadda ya shaida wa gidan talabijin na Channels.

Mai taimaka wa gwamnan ya ce gwamnatin jihar za ta tabbatar da hukunta waɗanda ke da alaƙa da wannan mummunan lamari.

Ya ce gwamnati tare da haɗin gwiwar jami’an tsaro na tattara bayanan da suka kamata domin tabbatar da an hukunta waɗanda suka aikata laifin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com