‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Mutane 3 a Abuja

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum uku a rukunin gidajen da ke bayan gidajen tsoffin sojojin ƙasar da ke rukunin gidaje na Kurudu a babban birnin tarayyar ƙasar Abuja.

Rahotonni daga ƙasar sun ambato daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojin ƙasar, Birgediya Onyema Nwachukwu na tabbatar da faruwar lamarin.

Birgediya Janar Nwachukwu ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:00 na daren ranar Alhamis

Mazauna rukunin gidajen sun ce maharan sun buɗe wuta a rukunin gidajen kafin daga bisani su arce da mutanen da suka yi garkuwar da su.

Cikin wata hira da ya yi da gidan talbijin na Channels a ƙasar, Birgediya Janar Nwachukwu ya ce dakarun soji sun garzaya rukunin gidajen a lokacin da suka samu kiran gaggawa dangane da abin da ke faruwa.

Ya ƙara da cewa jami’ansu na ci gaba da farautar maharan domin kuɓutar da mutanen.

Unguwar Kurudu na ɗaya daga cikin garuruwan da ke kan iyakar Abuja da jihar Nasarawa

A baya-bayan nan dai birnin Abuja na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, inda ke samun ƙaruwar ayyukan masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Ko a makon da ya gabata ma an samu ɓullar labarin garkuwa da wani mutum tare da ‘ya’yansa biyar a unguwar Bwari ke birnin Abujan, inda masu garkuwar suka kashe ɗaya daga cikin ‘ya’yan nasa bayan gaza biyan naira miliyan 60 a matsayin kuɗin fansa.

Batun ya ja hankalin mutane musamman a shafukan sada zumunta inda ‘yan ƙasar da dama suka riƙa tara kuɗaɗe a shafukan da nufin taimaka wa iyalan don kuɓutar da su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com