Hukuncin Kotun Koli: Zanga-Zanga ta ɓarke a Jihar Nasarawa

Zanga-zanga ta ɓarke a Lafia, jihar Nasarawa bayan hukuncin da kotun koli ta yanke da ya tabbatar da nasarar gwamna Abdullahi Sule a matsayin halastaccen gwamnan jihar a zaɓen da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na 2023.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an toshe hanyar Lafia zuwa Jos gaba daya yayin da masu zanga-zangar suka kunna wuta don hana matafiya da sauran masu amfani da hanyar.

Masu ababen hawa sun bi wasu hanyoyin don su samu su fita daga Lafia.

An kuma rufe shaguna da wuraren sana’a harda makarantu sakamakon zanga-zangar.

Kotu dai ta yi watsi da ƙarar da ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP David Ombugadu ya shigar inda yake ƙalubalantar nasarar Abdullahi Sule.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com