Ayyukan Haɗa Layin Waya a Najeriya na Samar wa ƙasar Maƙudan Kuɗi

 

Ayyukan haɗa layin waya ko simkad ta bunƙasa a Najeriya inda darajar harkar, ta kai naira biliyan 55, shekara ɗaya bayan Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta hana shigar da simkad cikin ƙasar.

Shugaban Hukumar, NCC, Farfesa Umar Danbatta ne ya sanar da haka lokacin taron da hukumar ta gudanar kan lamurran sadarwa a jihar Legas.

NCC ta ce “hana shigar da SIM-kad ɗin ya taimaka wajen ragewa hukumar nauyi na neman canjin kuɗaɗen ƙetare, ya kuma samar da wata hanyar kasuwancin da ta kai naira biliyan 55 ga kamfanonin da ke samar da SIM-kad a Najeriya.

Matakin kuma ya samar da ƙarin guraben aiki ga ‘yan ƙasa”.

Ɗanbatta ya kuma ce, “hukumar ta NCC na cikin manyan sassan da ke taimakawa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa, duba da irin jerin ci gaban ta sha samu”.

Ya ce, “babu tantama ɓangaren sadarwar Najeriya, ya taka muhimmiyar rawa wajen cire ƙasar daga koma-bayan tattalin arziki da ta taɓa fuskanta da kimanin kashi 12.45, a cikin wata uku na ƙarshen shekarar 2022”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com