Muna tare da ECOWAS Wajen Yin Allah-Wadai da Riƙe Shugaba Bazoum – Ministan Tsaron Birtaniya

 

Ministan tsaron Birtaniyar, James Heappey MP, ya gana da manyan shugabannin tsaron Najeriya domin ƙulla alaƙar da za ta kai ga tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu da za ta kai ga duba lamarin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar.

A lokacin ziyarar da ya kai Najeriya, Heappey ya gana da shugabannin tsaron ƙasar a ranar Laraba da suka haɗa da Hafsan Hafsoshin Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, da kuma Hafsan Sojan Ƙasa Laftanar Janar Taoreed Lagbaja.

Kazalika, ministan tsaron Birtaniyar samu ya ganawa da Ministan tsaron Najeriya, Abubakar Badaru, da kuma Ƙaramin Ministan Tsaro Bello Matawalle.

Ya kuma haɗu da Shugaban Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yama (Ecowas) Omar Touray, inda ya nanata shirin ƙasarsa na tallafa wa ƙungiyar a ƙoƙarin da take yi na ganin an ci gaba da tattaunawar diflomasiyya domin mayar da tsarin dimukuradiyya a Nijar.

Ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakan da Ecowas ɗin ke ɗauka a rikicin siyasar Nijar.

“Muna tare da Ecowas wajen yin Allah-wadai da riƙe Shugaba Mohamed Bazoum da iyalansa, da ma sauran jami’an gwamnati, musamman a irin halin da ake ci gaba da tsare su. Don haka muna kira da a gaggauta sakin su”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com