A ƙarshen Shekarar nan Matatar Man Patakwal Zata Ci gaba da Aiki – Ministan Fetur

 

Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta jaddata burinta na daina shigo da man fetur zuwa gida Najeriya nan da yan shekaru.

Ƙaramin ministan albarkatun fetur (Mai), Heineken Lokpobiri, ya ce a ƙarshen shekarar nan matatar Patakwal zata ci gaba da aiki.

Ya ce sauran matatun man Warri da Kaduna zasu biyo baya a shekara mai zuwa ga kuma matatar man Ɗangote.

Port Harcourt, Rivers – Gwamnatin Tarayya ta jaddada kudirinta na kawo karshen shigo da man fetur nan ba da daɗewa ba, inda ta ce ana kokarin dawo da aikin tace man fetur a cikin gida.

Ƙaramin ministan albarkatun man fetur (Mai), Sanata Heineken Lokpobiri, shi ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar duba aikin gyara matatar mai da ke Patakwal ranar Jumu’a.

Ministan ya kai wannan ziyara ne tare da takwaransa, karamin Ministan Man Fetur (Gas), Ekpeikpe Ekpo; da Babban Sakataren ma’aikatar albarkatun man fetur, Ambasada Gabriel T. Aduda

Sauran waɗanda suka raka ministan sun haɗa da shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL) da sauransu, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Yaushe matatun man Najeriya zasu ci gaba da aiki? Ya ce idan aka yi la’akari da irin ci gaban da aka samu a aikin gyaran matatar Patakawal, ana sa ran zata dawo aiki a watan Disamba na wannan shekara.

A rahoton Tribune, Ministan ya ce:

“Manufarmu ita ce mu tabbatar da cewa nan da ’yan shekaru masu zuwa, Najeriya ta daina shigo da mai. Daga abin da muka gani a nan yau, matatar Patakwal za ta fara aiki a karshen shekara.”

“Matatar Warri zata ci gaba aikin tace mai a karshen kwata na farko na shekara mai zuwa, sannan kuma matatar Kaduna za ta shigo cikin jirgin a karshen shekara mai zuwa.”

“Idan aka haɗa da matatar Dangote, za mu iya dakatar da shigo da mai cikin ƙasar mu, kuma ‘yan Najeriya za su ci gajiyar dakatar da biyan tallafin mai.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com