Mazaɓu a Legas Sun Fusata Kan Rashin Kai Masu Kayan zaɓe

 

Yayin da ake ƙoƙarin rufe shiga layin zaɓe ga masu zaɓe a wasu sassan Najeriya, wasu mazaɓu na kukan ba a kai musu kayan zaɓen ba.

Mazaɓar Amuwo Odofin da ke Legas, rumfa mai lamba 053 da 054 ba a kai kayan zaɓe a kan kari ba, inda mutane suka fusata, tare da zargin cewa ana ƙoƙarin yin maguɗin zaɓe.

Jami’an tsaro sun hallara a yankin inda suka buƙace mutanen da su kwantar da hankula.

Gabanin wannan wasu rumfunan sun riƙa fuskantar matsalar na’urar BVAS wadda ke ƙin ɗaukar zanen yatsa da kuma fuska.

An samu irin wannan matsalar a Maidguri a Jihar Borno, ka zalika Gwamnan Jihar Rivers Wike ma da farko sai da na’urar taƙi ɗaukar fuskarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here