Jami’ar Legas ta Rage Kuɗin Makaranta
Hukumomin Jami’ar tarayya da ke Legas sun bayyana rage kuɗin makaranta da na ɗakunan kwanan ɗalibai ga ɗaliban jami’ar.
Cikin makon nan ne dai ɗaliban jami’ar suka gudanar da zanga-zanga domin nuna adawa da tsadar kuɗin makaranta da jami’ar ta ƙara a zangon karatu na wannan shekara.
Read Also:
Matakin na zuwa ne bayan wata ganawa da aka gudanar tsakanin shugabannin jami’ar da na ƙungiyar ɗalibai ta ƙasa (NANS) da kuma shugabannin malaman jami’a.
Shugabannin daliban sun bukaci a sauya karin kudin makaranta da kudin wurin kwana na ɗalibai tare da maido da kungiyar dalibai a jami’ar.
Yayin da ta amince da rage kuɗaɗen makaranta da na masauki nan take, hukumomin jami’ar sun yi alkawarin fara aikin dawo da kungiyar dalibai a makarantar.