Ranar El-Clasico Tsakanin Barca da Real Madrid

 

Barelona za ta fara kece-raini a wasan hamayya da Real Madrid, ranar 28 ga watan Oktoba a gasar La liga.

Hukumar gudanar da gasar La liga ta sanar da ranar da aka sanya ne a Juma’ar nan.

Barcelona ce za ta fara karɓar baƙuncin Real Madrid a wasan hamayya na Clasico mai jan hankalin duniya a filin wucin gadi na Estadi Olimpic Lluis Companys, yayin da ake gyaran filinta na Camp Nou.

Real Madrid ta lashe duk wasanni huɗu da ta buga na La liga zuwa yanzu a bana, kuma ita ce a saman teburin gasar da maki 12, tazarar maki biyu tsakaninta da Barcelona.

Kafin manyan ƙungiyoyin biyu su fafata a Clasico, Real Madrid za ta kai ziyara Braga a gasar zakarun Turai ranar 24 ga watan Oktoba, Barcelona kuma za ta karɓi baƙuncin Shakhtar Donetsk a ranar 25 ga watan.

A kakar da ta gabata, sau biyar aka yi fafatawar Clasico, biyu a LaLiga, da kuma kofin zakaru na Spain wato Supercopa da kuma wasanni kece-raini a karawar dab da ƙarshe a gasar Copa del Rey.

Ƙungiyoyin biyu kuma sun gwabza a wasannin share fagen kaka, inda Barcelona ta yi nasara da ci 3-0 a Amurka. Manyan ƙungiyoyin biyu sun yi sabbin zubin ‘yan wasa a bana.

Madrid ta ɗauko ɗan wasan Ingila Jude Bellingham, wanda yanzu shi ne ke da yawan ƙwallaye a wasanni huɗu.

Akwai kuma ɗan wasan Spain Joselu da Fran García da Brahim Díaz da Arda Güle da mai tsaron raga Kepa Arrizabalaga.

Barcelona kuma ta yi cefanen Gündogan da Iñigo Martínez da Oriol Romeu da João Cancelo da João Félix

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com