Likitan Bogi ya Shiga Hannu Bayan Halaka Majinyaci Yayin Tiyata a Jihar Bauchi

 

Jami’an tsaro a jihar Bauchi sun kama wani Andrew Godwin da ake zargi likitan bogi kan halaka wani majinyaci yayin tiyata.

Rahotanni daga garin Bogoro sun bayyana cewa Godwin ya shafe shekaru yana yi wa mutane da ba su ankare ba tiyata kuma daga bisani su mutu.

Bincike ya nuna cewa Andrew yana da kemis na sayar da magunguna amma ba shi da lasisi ko satifiket na yi wa mutane tiyata.

Jihar Bauchi – Jami’an tsaro na hadin gwiwa ta Base 14 Boi a karamar hukumar Bogoro sun kama wani Andrew Godwin da ake zargin likitan bogi ne a Bauchi, Nigerian Tribune ta rahoto.

An kama wanda ake zargi likitan bogin ne, dan asalin jihar Nasarawa a ranar Lahadi saboda yin tiyata wacce ba ta yi nasara ba ta kuma yi sanadin mutuwar wani Joshua Haruna, dan shekara 45 mazaunin Gambar Lere a karamar hukumar.

Rahotanni sun nuna cewa wanda ake zargin, wanda ya shafe shekaru yana zaune a Gambar Sabon Layi a Tafawa Balewa ya dade yana haramtaciyyar kasuwancinsa kan mutane da ba su ankare ba.

Likitan bogin yana sayar da magunguna ne amma ba shi da wani satifiket na likitanci ko izini daga hukumomin da suka dace don ya rika tiyata.

An ce ya bude cikin wani majiyanci kuma ya bar shi a bude har ya goben ranan.

Mutanen gari sun ce Andrew ya dade yana yi wa mutane tiyata suna mutuwa Wani rahoto da ba a tabbatar ba ya ce Mr Andrew Godwin ya dade yana yi wa mutane tiyata wanda ba a samun nasara kuma daga bisani su mutu sakamakon tiyatar.

Jami’in JTF da ya kama shi ya ce sun kama ma’aikacin lafiyar na bogi sun kuma mika shi hannun yan sanda na Bogoro don zurfafa bincike.

An mika Andrew hannun yan sanda don cigaba da bincike An tura binciken zuwa caji ofis na yan sanda a Tafawa Balewa saboda Gambar Sabon Layi na karkashin karamar hukumar Tafawa Balewa ne yayin da Gambar Lere na karamar hukumar Bogoro.

Mamacin, kafin rasuwarsa shine tsohon shugaban gunduma ta APC, Boi C a karamar hukumar Bogoro kuma shugaban kamfen na Sanata Lawal Yahaya Gumau.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here