Lokaci ne Kawai Zai Nuna na yi Ritaya Daga Siyasa Ko Kada na yi – Gwamna Ganduje
Gwamnan jahar Kano Ganduje ya magantu kan yaushe zai yi ritaya daga harkokin siyasa.
Ya bayyana cewa, wannan lamari ne na lokaci, idan lokaci ya yi zai dakata amma ba yanzu ba.
Ya kuma shaida cewa, shi tsohon dan siyasa ne domin ya fara harkar siyasa tun shekarar 1978.
Gwamna Abdullahi Ganduje na jahar Kano ya ce mai yiwuwa ba zai yi ritaya daga siyasa ba nan kusa, duk da cewa ya shiga siyasa tun 1978, Daily Nigerian ta ruwaito.
Read Also:
Gwamna Ganduje ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida a yayin wata tattaunawa da mambobin kungiyar ‘yan jarida ta Kano a gidan gwamnati.
Wannan na zuwa ne biyo bayan sanarwar da Gwamna Aminu Masari na jahar Katsina, wanda ya bayyana zai fice daga siyasa a shekarar 2023, Nigeria Tribune ta ruwaito.
A nasa martanin, Mista Ganduje ya ce lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan. “A yanzu, ban gaji ba. Ko na yi ritaya ko kada na yi, lokaci zai nuna.
Bari in fada muku cewa na shiga siyasa tun shekarar 1978. “Don haka, ko da na ce zan yi ritaya, idanuna za su ci gaba da kallo, kuma kunnuwana za su ci gaba da ji,” in ji shi.