Najeriya na Bukatar Shugabanni da Zasu Hada Kan ‘Yan Kasar – Yemi Osinbajo

 

Mataimakin shugaban kasar Najeriya ya bayyana irin shugabannin da Najeriya ke bukata don ci gaban kasa.

Ya ce, dole ne a samu shugabanni masu son hada kan jama’a ba masu raba su matukar ana son kasar ta ci gaba.

Ya bayyana haka ne a jahar Legas a ranar Litinin yayin wata ziyara zuwa wata fadar sarautar gargajiya a jahar.

Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo ya ce Najeriya na bukatar karin shugabanni masu kwazo da shirye-shiryen hada kan kasar, Punch ta ruwaito.

Ya fadi haka ne a Legas a ranar Lahadi yayin wata ziyarar ban girma a fadar Oniru na Iruland, Oba Abdulwasiu Omogbolahan Lawal, a yayin bikin murnar nadin sarauta karo na farko.

Ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa mai taken, ‘Najeriya na bukatar shugabannin da suke shirye domin hada kan ‘yan Najeriya, in ji Osinbajo a wajen bikin cika shekara daya da nadin sarautar Oniru ’, wacce hadiminsa na yada labarai, Laolu Akande ya fitar.

Yayin da yake yaba wa Oba saboda jagorancinsa ga mazauna Iruland wadanda suka fito daga kabilu daban-daban, Osinbajo ya ce:

“Kasarmu tana bukatar dukkan shugabanni, shugabanni mafiya kyau, shuwagabannin da suka dace, shugabannin da suka shirya hada kan kasar.

“Legas karamar zuciya ta Najeriya, kowa na nan, idan abubuwa suka yi kyau a nan, abubuwa zasu yi kyau a kasar.

Yayin da yake yi wa Oba addu’ar samun nasara a kan karagar mulki, Mataimakin Shugaban kasar ya ce ci gaban masarautarsa da jama’arta ta tabbatar da ingancin shugabancin da yake bayarwa, wanda shi ne mizani don auna matsayin sarakunan gargajiya a kasar, Channels Tv tace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here