2023: Wannan Lokacin ne da Arewa za su Nuna Goyan Baya ga Tinubu – Kashim Shettima
Tsohon gwamnan jihar Borno da ke arewacin Najeriya Sanata Kashim Shettima, ya ce wannan lokacin ne da arewa za su nuna goyon baya ga jagorar jam’iyyar APC mai neman takarar shugabancin Najeriya Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Sanata Shettima ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa ta musamman da ya yi da jaridar Daily Trust.
Read Also:
Gwamnan wanda na daya daga cikin gwamnonin ANPP uku da suka koma APC bayan rugujewar tasu jam’iyyar lokacin gamayyar da aka yi ta jam’iyyu a zaben 2015, ya jaddada cewa wannan lokaci ne da ya kamata a biya Tinubu wahalar da ya yi na cika dogon burin shugaban Najeriya na yanzu Muhammdu Buhari.
An yi amannar cewa Buhari da Tinubu sune mutum biyu da suka fi kowa mahimmanci a tafiyar APC a 2013, wanda gamayyarsu ta kai ga Buhari ya samu shugabancin Najeriya.
“Babu shakka Buhari na da farin jini a Arewa. Akwai mabiyansa kusan miliyan 15 a yankin. Amma hakan bai sanya ya zama shugaban kasa ba sai da ya hada hannu da yan siyasar sauran bangarorin kudanci da sauran yankuna aka sauya masa fasali tukunna ya zama shugaban kasa a 2015,” in ji Shettima.