‘Yan Bindiga na ci Gaba da Kai Farmaki Jahar Neja

Rahotanni sun kawo cewa yan bindiga na ci gaba da kai hare-hare a wasu garuruwa a jihar Neja.

An tattaro cewa harin wanda suka fara kaddamarwa a yammacin ranar Asabar yana nan yana ci gaba da gudana har yanzu haka.

Shugaban karamar hukumar Magama, Safiyanu Ibeto, ya tabbatar da hare-haren.

Neja – ‘Yan bindiga na ci gaba da kai farmaki a garuruwan Zoma, Yangalo, Masamagu, Atabo da sauran garuruwan da ke makwabtaka a karamar hukumar Magama ta jihar Neja.

Mummunan harin ya tursasa mazauna kauyukan tserewa zuwa garin Kontagora, hedikwatar karamar hukumar Kontagora.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa farmakin wanda suka fara kaiwa a yammacin ranar Alhamis na ci gaba da gudana har yanzu haka, inda aka ce mutane da dama sun mutu sannan an yi garkuwa da wasu da dama.

Har ila yau rahoton ya nuna cewa wasu da dama sun jikkata a harin yayin da wasu suka tsere daga gidajensu.

Da aka tuntube shi domin jin ta bakinsa, kakakin rundunar yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya yi alkawarin sake kira amma zuwa yanzu bai aikata hakan ba.

Sai dai shugaban karamar hukumar Magama, Safiyanu Ibeto, ya tabbatar da hare-haren.

Wasu mazauna kauyukan da suka zanta da Daily Trust a ranar Lahadi, 13 ga watan Fabrairu, sun ce maharani suna ta kai hari tun daga ranar Alhamis ba tare da hukumomin tsaro sun shiga lamarin ba.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Ko da muka fara masu, basu kawo dauki ba. An barmu a hannun yan bindiga.”

Wata dattijuwar mata, Khadijah Abdullahi, ta ce yaranta aurarru mata su biyu wadanda ke da yara biyar da uku na cikin wadanda aka yi garkuwa da su.

Wata da ta tsallake rijiya da baya a harin, Safiya Abdullahi, ta ce:

“Da na hango su, sai na gudu na haye kan tsauni. Ban san cewa wasu daga cikinsu sun gan ni ba lokacin da nake boyewa. Na lullube kaina da hijabi. Suna a kan kimanin babura 30. Cikin ikon Allah, sai suka bukaci na gaggauta barin wajen. Ta haka ne na tsira.”

Wani da ya tsere, Shamsudeen Abdulmalik Atabo, ya ce maharani sun fara kai hari a garuruwa uku da misalin 12:00 na rana kuma har zuwa yammacin Asabar suna chan.

Ya ce:

“Matar yayana na cikin wadanda aka yi garkuwa da su. Yanzu haka ina a Kontagora inda nake zama tare da yan uwana.”

Daily Trust ta tattaro cewa har yanzu yan bindigar na nan suna kai hari a Yangalo, babban garin da suka tara dabobbin sata. Mazauna kauyukan da suka tsere suna samun mafaka a Usubu, wani yanki na Kontagora.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here