Ƙungiyar Ma’aikatan ƙera Motocin Amurka Sun Shiga Yajin Aiki
Ma’aikata fiye da 10,000 na kamfanonin ƙera motoci mafi girma a Amurka, sun shiga yajin aiki, bayan gaza cimma daidaito a kan ƙarin albashi da inganta walwalarsu.
Ƙungiyar ma’aikata ƙera motocin Amurka sun dakatar da ayyuka a kamfanoninsu uku da suka haɗar da General Motors da Ford da kuma Stellantis.
Read Also:
Ƙungiyar ta buƙaci a yi musu ƙarin kashi 40 cikin 100 a albashinsu. Tun shekara ta 2008 rabon da a waiwayi waɗannan ma’aikata da sunan ƙarin albashi.
Rikici tsakanin ma’aikatan da kamfanonin, yana iya haifar da tashin farashin motoci, ya kuma haifar da cikas a masana’antar ƙera motocin.
Shugaban ƙungiyar ma’aikatan Shawn Fain ya shaida wa BBC cewa yanzu ya rage wa kamfanonin su shawo kan wannan matsala.
“Da zarar sun fara kula da ma’aikatansu, matsalar za ta zama tarihi.”