Yadda Za’a Magance Matsalar Tsaro – Ahmad Lawal ga Gwamnatin Tarayya

Dr. Ahmad Lawan ya gabatar da wata mafita ga gwamnatin tarayya don magance lamarin Boko Haram.

Shugaban majalisar dattawan da yake rokon gwamnati ya bayyana cewa yanzu ne lokacin da ya dace a sauya fasalin tsaron kasar.

Lawan ya yi kiran ne a lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa zuwa jihar Borno kan mummunan kisan kiyashi da aka yi wa manoman shinkafa 43.

Biyo bayan kisan manoma 43 a jihar Borno wanda yan Boko Haram suka yi, an bukaci gwamnatin tarayya da ta duba yiwuwar sauya tsarin tsaro a Najeriya.

Dr. Ahmad Lawan ya yi kiran ne a ranar Litinin, 30 ga watan Nuwamba, lokacin da ya jagoranci tawagar Shugaban kasa domin yi wa gwamnati da mutanen Borno jaje kan mummunan lamarin, jaridar The Sun ta ruwaito.

A cewar Lawan, tsarin da ake dashi a kasa baya aiki, inda ya kara da cewa gwamnati na bukatar samun sabbin manufofi da kuma ganin yadda tsarin tsaron zai inganta.

Shugaban majalisar dattawan da yake magana da manema labarai a Maiduguri, babbar birnin Borno, bayan ziyarar jajen zuwa Zabarmari, ya kuma bayyana cewa akwai bukatar sabonta rundunar tsaro.

Ya jaddada cewa ya kamata kashe-kashen da ake yi ya tursasa Shugaban kasar sake tsarin tsaron kasar, cewa akwai bukatar samun sauyi a yanzu.

Lawan ya kuma bayyana cewa rundunar soji da sauran hukumomin tsaro a kasar na bukatar karin kudi. Ya ce akwai bukatar daukar karin ma’aikata a hukumomin tsaro.

Shugaban majalisar dattawan ya ce maimakon gina hanyoyi da sauran kayayyakin more rayuwa a inda mutane basu da tsaro, kamata yayi a zuba kudaden wajen yaki da tsaro.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here