Ya Kamata a Magance Matsalar Tsaro Kafin Zaɓen 2023 – Mike Ejiofor

Wani tsohon Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS yace matuƙar Najeriya ta cigaba da tafiya a haka to zaɓen 2023 ma bazai yuwu ba.

Tsohon Daraktan yace yakamata gwamnati ta farka, ta magance matsalar tsaro tun kafin lokacin zaɓen ya yi.

Daraktan ya goyi bayan kiraye-kirayen da akeyi na sake fasalta ƙasar nan, a cewarsa hakan zai taimaka wajen warware wasu matsalolin Wani tsohon Daraktan hukumar tsaro ta farin kaya DSS, Mike Ejiofor, ya yi gargaɗin cewa zaɓen dake ƙaratowa na 2023 bazai yuwu ba sabida ƙara taɓarɓarewar da harkar tsaro ke yi a ƙasar nan.

Lokacin da yake jawabi a wata tattaunawa da Channels TV cikin shirin ‘Sunrise Daily’, Ejiofor ya yi kira ga gwamnatin tarayya ta gaggauta kawo ƙarshen matsalar.

Tsohon Daraktan yace Matuƙar ba’a daƙile matsalar nan kafin zaɓen 2023, kuma ba’a warware dukkan ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a yankuna daban-daban na ƙasar nan ba, to babu ta yadda za’ayi zaɓe ya yuwu a wannan yanayin.

Mine Ejiofor ya ce: ‘Idan bamuyi da gaske mun magance matsalar nan ta tsaro ba, bamu warware matsalar ba a dukkan yankunan da abun ya shafa a ƙasar nan, to ina mai tabbatar muku bazai yuwu a gudanar da zaɓe ba.”

“Za’a samu hargitsi da tarzoma a ƙasar nan, yakamata mu yi duk abinda ya dace mu warware matsalolin nan kafin shekarar 2023.”

“Mu ajiye maganar zaɓe a gefe guda, matuƙar muka cigaba da tafiya a haka to zaɓen ma bazai yuwu ba.”

Duk da jerin gwanon matsalolin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta, Ejiofor ya goyi bayan kiran da ake na sake zama domin gyara fasalin ƙasar nan.

Ya ce wannan aikin na gayaran fasalin ƙasa zai taimaka sosai wajen ganin an warware da yawa daga cikin matsalolin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here