ASUU: Abinda Za’ayi a Najeriya Don Magance Matsalar Yajin Aiki

Kungiyar malaman jami’o’in Najeriya, ASUU, ta bada shawarwari kan yadda za a kawo karshen yawan yaji aikin yi.

Kungiyar ta ce ya zama dole a kafa doka da zata hana masu rike da mukaman siyasa da yaransu zuwa kasashen waje karatu ko asibitoci neman magani.

Ta kuma ce idan ba gwamnati ta canja halinta ta mayarda hankali wurin gina ilimi a kasar ba da wuya a kawo karshen yajin aikin.

Ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta ce hanya guda da za a magance yawan yajin aiki ita ce kafa doka da zata haramtawa masu rike da mukamai a gwamnati tura yaransu karatu kasashen waje.

Shugaban ƙungiyar na shiyya, Farfesa Olufayo Olu-Olu, cikin wata sanarwa ya ce hakan zai taimaka wurin gina ɓangaren ilimi a ƙasar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

“Masu mulki da abokansu duk yaransu na karatu a ƙasashen ƙetare, don haka ba su damu da kawo ƙarshen yajin aikin ASUU ba tunda mulkin ya zama sana’a ne a wurinsu ba yi wa al’umma hidima ba.

“Idan ba mun kafa doka kan wasu abubuwa biyu ba, ba zamu rabu da wannan matsalar ba.

na farko, dokar da zata tilastawa masu riƙe da muƙaman siyasa da yaransu yin karatu daga frimari har makarantun gaba da sakandare a Najeriya.

“Na biyu, doka ta zata haramtawa masu riƙe da mukaman siyasa da iyalansu zuwa kasashe waje neman magani.

Idan an kafa wannan dokokin biyu, da yiwuwar mu fara ganin ƙarshen yajin aikin ASUU a ƙasar nan.

“Idan har gwamnati bata yi abinda ya dace ba (an saki kudaden don gina makarantun mu, an biya allawus ɗin mu da wasu sauran abubuwa) zamu cigaba da wannan gwagwarmayar,” a cewar wani bangare na sanarwar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here