Gidauniyar Aminu Magashi ta Bada Tallafin Keken Guragu a Kwalejin Sa’adatu Rimi
Gidauniyar ta Aminu Magashi ta bada tallafin keken Guragu a kwalejin sa’adatu Rimi Dake jihar kano
Hakan ya biyo bayan wani malami dake koyarwa a kwalejin mai suna malam inuwa ishaq ya bayar da korafi akan dalibai masu kokarin karatu a kwalejin amma suna fama da lalurar kafa.
Da take jawabi,Daya daga cikin hadiman Gidauniya Hannatu Suleiman Abba tace, Gidauniyar ta saba tallafawa masu bukata ta musamman a fannonin da suka shafi ilimi,lafiya,da bada jari ga masu kasuwanci inda tace Haka ne yasa Gidauniyar ta bude wani bangare domin tallafawa masu bukata ta musamman da marasa karfi a cikin al’umma Wanda ake ce mata vulnerable peoples support and initiative.
Read Also:
Ta kara da cewa, gidauniyar ta cigaba da kawo wa kwalejin da sauran guraren da masu bukata ke bukatar tallafin a duk fadin jahar da kuma kasa baki Daya.
Cikin jawabin da shugaban makarantar sa’adatu Rimi farfesa yahaya bunkure ya bayyana cewa, abun Alfahari ne da koyi game da abunda Gidauniyar tayiwa makarantar duba da cewa ba a taba samun wata kungiya da ke karkashin wani mai kudi ba ta kawo wa makarantar Tallafin kayayyakin karatu ko kaya ba.
Farfesa bunkure ya bayyana cewa, Gwamnati na kokari sosai wajen ganin karatun masu bukata ta musamman ya cigaba inda ya cewa ya kwashe sama da shekara 20 yana koyar da fannin a makarantar, yana da kyau masu kudi a cikin al’umma su dinga kawo Tallafin a wannan bangaren domin masu wannan lalurar su samu zurfin karatu da kwarewa.
Taron ya samu hallacin rajistara na makarantar, mal saminu bello harbau shugaban sashin masu koyar da masu bukata ta musamman,mal Suleiman gezawa ,mal ishaq inuwa, shugabar kungiyar YOSPIS zainab nasir Ahmad, Aisha Ibrahim Danpullo ,da sauran malaman kwalejin.