Rikici da Matarsa: Magidanci ya Rasa Ransa Sakamakon Shan Guba

 

Vandu Weida mai shekaru 29 da yara 3 ya halaka kan sa bayan ya sha guba a ranar Talata.

Hakan ya biyo bayan wani rikici wanda ya janyo tashin hankali tsakanin sa da matar sa.

Rikicin ya auku ne a Mildu Central dake karamar hukumar Madagali a jahar Adamawa.

Jahar Adamawa -Wani magidanci mai suna Vandu Weida, mai shekaru 29 ya riga mu gidan gaskiya sakamakon gubar da ya sha.

Lamarin ya faru ne a Mildu Central, a karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa ranar Talata.

Vandu, mai yara 3 ya samu hayaniya ne tsakanin sa da matar sa wanda har ya koma gagarumin fada.

Kamar yadda Punch ta rawaito, wani ganau ya ce yayin fadan, Weida ya bayyana wa matar sa cewa ya gaji da ita da duniyar ma baki daya don haka ya gwammaci ya mutu ya bar ta da yaran.

Bayan fadan, mutumin ya kasa jurewa hakan ya sa ya sha guba daga baya a ka gan shi a kasa yana numfashi da kyar.

Likitoci sun tabbatar gubar ta lalata ma sa hanji

Anyi gaggwar wucewa da shi babban asibitin Mubi inda aka tabbatar da cewa gubar da ya sha ta lalata ma sa hanji.

Kamar yadda Punch ta rawaito, Kakakin rundunar ‘yan sandan jahar, DSP Suleiman Nguroje ya ce bai san komai akan lamarin ba amma ya yi alkawarin bincike a kan lamarin a ofishin ‘yan sanda na Madagali.

Har lokacin cike rahoto be nemi wakilin The Punch ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here