Mahautan Jahar Kwara Sun Koka da Tsadar Shanu a Jahar

 

A jahar Kwara, mahauta sun koka kan yadda shanu suka kara tsada sakamakon wasu dalilai.

Sun koka cewa, a yanzu ba sa iya yanka shanu saboda irin asarar da suke tafkawa idan suka yi.

Sun kuma ce, ba sa iya zuwa Arewa domin sayen shanu saboda yawaitar matsalar rashin tsaro a yankunan.

Kwara – Rahoto daga Daily Trust ya ce, mahauta a jahar Kwara sun daina yanka shanu sakamakon tsadar kayan masarufi.

Wannan lamarin ya haifar da karancin nama a duk kasuwanni a Ilorin, babban birnin jahar.

Wani mahauci a Kasuwar Mandate da aka fi sani da Alfa ya ce ba za su iya samun naman da za su saya daga dukkan mahautan da ke Ilorin ba.

Wani mahauci, Abu Olowo, wanda ke gudanar da kasuwancin nama a Irewolede ya ce:

“Naman ya yi tsada. Muna sayar da kilo N2,500 sabanin N1,500 da yake a da. Yanayin girman saniya, yanayin girman asaran da za a tafka kuma sabanin mu da muke siyarwa a kilo, lamarin ya fi muni ga wadanda ke cikin kasuwanni.”

Sakataren Mahautan Saraki, Akerebiata, Alhaji Oba Elegede, ya danganta lamarin da tsadar shanu.

A cewarsa: “Kasuwar babu ita ma saboda tsadar shanu.

Ta yaya za ka bayyana halin da saniya N100,000 ta koma N250,000? “Ba za mu iya saye daga Arewa da nisa kamar Yobe da Maiduguri ba inda muke samun shanu masu arha saboda rashin tsaro.

Muna zagaye kasuwannin shanu da ke kusa da Kwara, Ilesha Baruba, Kaiama, Ajase, Share, Bode Saadu, Jebba da Igbeti.

“A karshe lokacin da wasu yaran mu suka yi balaguro zuwa jhar Neja, an yi garkuwa da biyu daga cikin su kuma mun biya kudin fansa don tsira da rayukan su.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here