Bai Kamata Majami’u su Saka Hannu Cikin Al’amuran Zabe ba – Shugaban CAN
Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya Dakta Daniel Okoh, ya umarci shugabannin Kiristoci da majami’un da ke fadin kasar da kada su shiga harkokin zaben kasar.
Jaridar punch a Najeriya ta ambato mista Okoh na umartar ‘yan kasar da su yi nazari mai zurfi wajen zabar wanda zai jagoranci kasar a zaben shugaban kasar da ke tafe.
Read Also:
Mista Okoh ya yi wannan kira ne a birnin Onitsha lokacin bikin zagayowar ranar haihuwar shugaban Cocin Mission International, Bishop Paul Nwachukwu.
Ya ce ya yi imanin cewa akwai muhimmiyar rawa da majami’u za su taka wajen samar da shugaban kasar na gaba.
”Bai kamata majami’u su saka hannu cikin al’amuran zabe ba, to amma ya wajaba a kansu su tabbatar da cewa sun taimaka wa mutane wajen zabar shugaban da ya dace, saboda makomar kasar na hannunsu”, in ji shi.