Gwamnatin Tarayya ta Bankaɗo Kadarori 14 Mallakar Abba Kyari

 

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bankaɗo wasu kadarori 14 mallakar tsohon shugaban rundunar tattara bayanan sirri ta hukumar ‘yan sandan kasar DCP Abba Kyari.

Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa kadarorin sun hadar da manyan kantunan sayayya, da gidaje, da filin wasan polo, da filaye tare kuma da gonaki.

An zargi Kyari da kin bayyana kadarorin nasa dake wurare daban-daban a birnin Tarayya, Abuja da birnin Maiduguri na jihar Borno.

An kuma gano sama da naira miliyan 207 da euro 17,598 a asusun ajiyarsa na bankunan GTB, da UBA, da kuma bankin Sterling.

A cikin sabbin tuhume-tuhume 24 da daraktan hukumar gabatar da kara da ayyukan shari’a ya gabatar, ya ce babban lauyan gwamnatin kasar ya yi zargin cewa Abba kyari ya ki bayyana wa hukumomi wasu ƙaɗarorin nasa.

Haka kuma gwamnatin tarayya ta shigar da wasu tuhume-tuhume daban guda 24 a kan Sunday Ubua, tsohon mataimakin Abba Kyarin, wanda shi ma tuni aka dakatar da shi.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here