Bayan Kama ƙwayoyi a Gidansa: Majalisa ta Kafa Kwamitin Binciken Sanata

 

FCT, Abuja – Majalisar dattawa ta ɗauki mataki kan zargin da hukumar NDLEA ta yi wa Sanata Oyelola Yisa Ashiru na samun ƙwayoyi a gidansa.

Majalisar dattawan ta kafa kwamitin wucin gadi da zai binciki zargin da hukumar ke yi wa sanatan wanda shi ne mataimakin shugaban masu rinjaye.

Majalisar dattawan ta dauki matakin ne a ranar Talata bayan da Sanata Ashiru ya gabatar da wani ƙudiri, cewar rahoton jaridar The Cable.

NDLEA ta zargi Sanata da harkar ƙwayoyi

Tun da farko dai hukumar NDLEA ta ce ta gano kwayoyi a gidan Sanata Ashiru kuma ta kama wasu hadimansa guda biyu a shekarar 2023, zargin da ya musanta.

Zargin na NDLEA ya zo ne bayan sanatan mai wakiltar Kwara ta Kudu ya ce hukumar ita ce “hukumar gwamnati mafi cin hanci da rashawa” a ƙasar nan.

Yayin da yake magana a zauren majalisar dattawa, Sanata Ashiru ya ce NDLEA na ƙoƙarin hana shi magana a matsayinsa na sanata kan al’amura ta hanyar jifarsa da zargin da bai da tushe.

“Ina so in tabbatar da cewa ban san menene tabar wiwi ba, ba na shan barasa. Domin kariyata da ta sauran Sanatoci, dole ne mu yi wani abu game da wannan.”

Sanata Oyelola Yisa Ashiru

Majalisa ta kafa kwamitin binciken Sanata

Da yake mayar da martani, shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya ce akwai buƙatar wani kwamitin wucin gadi da zai binciki lamarin cikin tsanaki, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Daga ƙarshe an naɗa Enyinnaya Abaribe, Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu a matsayin shugaban kwamitin wucin gadi.

Ana sa ran kwamitin zai miƙa rahotonsa cikin mako guda.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here