Magance Matsalar Tsaro: Majalisar Dattijai Zata Tura Shugabanninta Don Ganawa da Shugaba Buhari

 

Bayyanar cewa kungiyar Boko Haram na kara kusantowa kusa da Abuja ya sa wasu jiga-jigan ‘yan majalisar dattijan kasar shiga halin fargaba.

Sanatocin da suka firgita sun yi kira ga shugaban kasa da ya gaggauta daukar matakan ceto babban birnin tarayyar kasar nan daga fadawa hannun masu tayar da kayar baya.

Tuni, wata tawaga daga majalisar dattijai ke shirin ganawa da shugaban kasar domin bayyana bukatunsu a fili Sanatocin Najeriya a ranar Talata, 27 ga Afrilu sun bayyana tsoron cewa mayakan Boko Haram na iya mamaye babban birnin kasar, Abuja.

Sanatocin sun bayyana damuwar su a yayin zaman majalisar bayan wani kudiri, wanda sanata Musa Sani daga jahar Neja ya gabatar.

Sani, sanatan da ke wakiltar yankin Neja ta Gabas, ya sanar da takwarorinsa cewa tafiyar awa biyu ne kadai ke tsakanin yan ta’addan da Abuja.

Kalaminsa:

“An watsar da mazaunan wadannan sassan jahar da ke fama da yaki kuma an barsu daga su sai halinsu wanda hakan ya tilasta masu zama cikin mummunan bakin ciki.”

Ya kara da cewa garuruwa 42 da ke fadin kananan hukumomin biyu na Shiroro da Munya sun fada karkashin ikon Boko Haram zuwa yanzu inda mazauna kauyuka kusan 5,000 suka rasa matsugunansu a cikin kwanaki uku da suka gabata.

Da yake bayar da gudummawarsa ga kudirin, tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ike Ekweremadu, a cikin nasa jawabin ya ce gwamnatin da Buhari ke jagoranta ta rasa cancantar ta na jagoranci.

Kalaminsa:

“Duk gwamnatin da ba za ta iya kare rayukan mutane ba to ta rasa cancantar ta. Muna buƙatar yin wani abu game da wannan kuma cikin sauri. Idan akwai bukatar mu rufe jahar Neja ko majalisar dattawa domin neman mafita, toh mu yi hakan.” A matsayin hanyar magance matsalar, majalisar dattijai ta yanke shawarar tura shugabanninta don ganawa da Shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban majalisar dattijai, Ahmad Lawan, ya bayyana cewa zai jagoranci sauran manyan shugabannin majalisar dokokin, domin ganawa da shugaban kasa.

Hakanan majalisar ta yanke shawarar kiran sabbin hafsoshin da aka nada domin yi musu bayani kan matakan da aka dauka na kawo karshen lamarin. Sai dai ba a sanar da ranar yin hakan ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here