Karin Kudin Makaranta: Majalisar Dokokin Jahar Neja ta Sammaci Shugabannin Jami’ar IBBUL
‘Yan majalisa sun ce kara kudin makaranta a jami’ar IBB bai dace ba Kakakin majalisar ya bukaci.
shugabannin makarantar suyi masa bayani Daliban jami’ar sun bayyana rashin amincewarsu da wannan sabon kari.
Majalisar dokokin jahar Neja ta sammaci shugabannin jami’ar Ibrahim Badamasi Babangida, IBBUL, Lapai, su bayyana gabanta domin bayanin dalilin kara kudin makarantar.
Read Also:
Wannan sakon sammaci ya biyo bayan tattaunawar da yan majalisar suka yi bayan Hanarabul Mohammed Haruna, mai wakiltar mazabar Bida II ya gabatar da lamarin a zauren majalisa.
Haruna ya ce wannan abin takaici ne musamman a lokaci irin wannan da mutane ke cikin halin yunwa, rahoton DailyNigerian.
Dan majalisan ya ce wannan abu da jami’ar tayi zai tilastawa dalibai ajiye karatu ko kuma shiga ayyukan alfasha.
Kakakin majalisar, Abdullahi Bawa, yayin jawabi a majalisa ya umurci shugabannin jami’ar gaba daya su gurfana gaban kwamitin majalisar don bayanin dalilinta.