Tsohon Gwamnan Jahar Kano, Dominic Oneya ya Riga mu Gidan Gaskiya

 

Tsohon gwamnan jahar Kano lokacin mulkin Soja, Dominic Oneya, ya rigamu gidan gaskiya yana mai shekara 73.

Hadimin gwamna Abdullahi Ganduje, Abubakar Aminu Ibrahim, ya bayyana haka a jawabin da ya sake ranar Alhamis.

Majiyoyi daga iyalansa sun bayyana cewa tsohon Sojan ya mutu ne a gidansa dake Agbarho karamar hukumar Effurun ta jahar Delta, rahoton Tribune.

Sun kara da cewa ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiya saboda ko makon da ya gabata ya tafi Abuja.

Oneya, ya kasance gwamnan Kano tsakanin Agustan 1996 da Agustan 1998 lokacin mulkin marigayi Janar Sani Abacha.

Bayan haka kuma, ya kasance gwamnan jahar Benue tsakanin Agustan 1998 da Mayun 1999.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here