Majalisar Dattawa ta yi Jimamin Kisan Gillar da ‘Yan Bindiga Suka yi wa Jama’a fiye da 120 a Jahar Sokoto
Majalisar dattawa ta yi shiru na minti daya a matsayin jimamin kisan gilla kan jama’ar Sokoto fiye da 120.
Yan bindigar sun kai mummunan hari kasuwar Goronyo da ke jahar Sokoto a ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoba, inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi.
Dan majalisa mai wakiltan Sokoto ta gabas, Sanata Ibrahim Gobir, ne ya koka kan ayyukan yan ta’addan a garuruwan da ke yankin a zauren majalisar.
Majalisar dattawa a ranar Laraba, 10 ga watan Nuwamba, ta yi shiru na minti daya domin jimamin kisan gillar da yan bindiga suka yi wa jama’a fiye da 120 a kasuwar Goronyo da ke jahar Sokoto.
Dan majalisa mai wakiltan Sokoto ta gabas, Sanata Ibrahim Gobir, ya ja hankalin majalisar zuwa lamarin ta a lokacin da aka fara zaman, rahoton Punch.
A cewar dan majalisar, maharan sun yi wa mutanen da lamarin ya ritsa da su kisan gilla ne a ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoban 2021.
Da yake bayani, Gobir ya ce:
“A ranar Lahadi, 17 ga watan Oktoba, an kai hari kasuwar Goronyo, sannan aka kashe fiye da mutane 120.
Read Also:
“Yan ta’addan sun isa kasuwar sannan suka fara harbin duk mutumin da suka gani a kasuwar.”
Ya bayyana cewa yan bindiga sun dorawa mazauna kauyuka bakwai a wannan karamar hukumar biyan haraji tsakanin naira miliyan 1 zuwa miliyan 20.
Gobir ya bayyana kauyukan da lamarin ya shafa a matsayin Kwarangamba, Garki, Danadua, Katuma, Kurawa da Dama.
A ruwayar Daily Trust, ta ce dan majalisar ya koka kan cewa rashin cika bukatun yan bindigar a yankunan da abun ya shafa ya yi sanadiyar kisan jama’a da dama.
Gobir ya nuna gajiya cewa duk da yawan rokon da ake wa hukumomin tsaro a kan su kawo agaji ga garuruwan da abun ya shafa, babu abun da sojoji da yan sanda suka yi don shiga lamarin.
Ya ci gaba da bayyana cewa gazawar sojoji wajen kaiwa mazauna yankunan agaji ya baiwa yan ta’addan karfin gwiwar nada wakilansu a matsayin hakimai a wasu yankunan karamar hukumar Sabon-Birni.
Ya kara da cewa:
“A yanzu yan ta’addan na nada hakimansu a wasu yankunan karamar hukumar Sabon-Birni.
“A Gangara, sun maye gurbin hakimin garin da Dan Bakkolo, mataimakin sanannen dan ta’adda mai suna Turji.
“A Makwaruwa, sun nada Dan Karami wanda yake dan ta’adda ne a matsayin Maigari.”